Rahoton ya yi nuni da cewa, adadin kudin da kasashen da suka fi samun bunkasuwar tattalin arziki suka samu a zahiri daga aikin kawo albarkar cikin gida a cikin watanni uku na karshen shekarar da ta gabata ya samu raguwa da kashi 7.5 cikin kashi 100,wadda ba a taba ganin irinta ba a tahiri. Kasar Amurka wadda ta kasance mafarin haifar da rikicin hada-hadar kudi na duniya a wannan gami za samu raguwar tattalin arziki da kashi 2.8 cikin kashi 100 a wannan shekara, amma tana sa ran samun farfadowa a tsakiyar shekara mai kamawa ; Kazalika, kasashen Japan, da Burtaniya, da Canada, da kuma na yammacin Turai suna biye da ita.
Aminai 'yan Afrrika, ko kuna sane da cewa, kasashen da suka fi samun bunkasuwar tattalin arziki su ma sun samu tabarbarewar tattalin arziki bisa babban mtaki sakamakon koma bayan harkokin cinikayya da karancin kudade. Ana kyautata zaton cewa, kasashe masu tasowa na Asiya za su dage ga samun bunkasar tattalin arziki bisa ingizawar da kasashen Sin da India suke yi, wato ke nan saurin bunkasuwar tattalin arzikinsu a wannan shekara zai kai kashi 4.8 cikin kashi 100, a shekara mai zuwa ma da kashi 6.1cikin kashi 100. Kasar Sin za ta rage saurin bunakasuwar tattalin arzikinta a bana da badi, amma gwamnatin kasar Sin za ta dauki wassu tsauraran matakai na sa kaimi ga harkokin kudi da kuma sasanta manufofin kudi da take aiwatarwa yayin da take kara zuba makudan kudade a fannin manyan ayyukan giggina kayan more rayuwar jama'a. Ko shakka babu, har ila yau, tattalin arzikin kasar Sin na samun karfin ingantuwa ; Ban da wadanan kuma, kasashen Afrika da na Gabas ta Tsakiya har da na Latin-Amurka su ma za su soma farfado da tattalin arzikinsu a shekara mai kamawa.
1 2 3
|