Batu na biyu shi ne wace jam'iyya ce za ta zama jam'iyya mafi girma da ke adawa da gwamnatin kasar Afirka ta Kudu? Ko da yake an riga an kawo karshen tsarin nuna wariya cikin tsawon shekaru 15, duk da haka bakaken fata da fararen fata su kan sha bamban sosai lokacin da suke zabar jam'iyyun da za su goyi bayansu. Bakaken fata da yawansu ya kai kusan kashi 80 cikin kashi dari suna goyon bayan jam'iyyar ANC, kuma wannan shi ne muhimmin dalilin da ya sa Jam'iyyar DA da yawancin masu goyon bayanta fararen fata ne ba ta iya raunana matsayin Jam'iyyar ANC.
Amma sakamakon kafuwar Jam'iyyar COPE a karshen shekarar da ta gabata, halin siyasa da kasar Afirka ta Kudu ke ciki ya samu canzawa sannu a hankali. Kila wasu bakaken fata da ba su gamsu da harkokin gudanarwa da Jam'iyyar ANC ke yi da kuma wasu fararen fata da halin da Jam'iyyar DA ke ciki ya bata ransu sosai za su goyi bayan Jam'iyyar COPE da ke daga tutar "yaki da cin hanci da rashawa".
1 2 3
|