A ran 22 ga wata, za a shirya babban zabe a karo na hudu a kasar Afirka ta Kudu bayan da ta kawo karshen tsarin nuna wariya. Bisa manyan fannoni, za a iya gano cewa, Jam'iyyar ANC da ke kan karagar mulkin kasar za ta cimma nasara cikin sauki a yayin zaben a wannan karo, kuma shugaban Jam'iyyar ANC Jacob Zuma zai zama sabon shugaban kasar. Amma ya zuwa yanzu da akwai batutuwa uku da ba za su tabbata ba sai dai bayan da aka kammala zaben.
Batu na farko shi ne ko Jam'iyyar ANC za ta iya ci gaba da samun kujerun da yawansu ya kai kashi 2 cikin kashi 3 a cikin majalisar dokoki ta kasar Afirka ta Kudu. A matsayinta na jam'iyyar siyasa mafi muhimmanci da ta jagoranci kasar Afirka ta Kudu wajen kawo karshen tsarin nuna wariya, tun daga shekara ta 1994, ko da yaushe jam'iyyar ta kan samu kujeru masu yawa a cikin majalisar dokoki ta kasar, kuma a shekara ta 2004, ta samu kujerun 279 wadanda yawansu ya zarce kashi 2 cikin kashi 3, ta haka ta mallaki cikakken iko na gyara tsarin mulkin kasar.
Amma a cikin babban zaben da za a shirya a shekarar da ake ciki, sakamakon janye jiki da wasu dattijai na Jam'iyyar ANC da ke goyon bayan tsohon shugaban kasar Mr. Thabo Mbeki suka yi daga jam'iyyar, da kuma kafa Jam'iyyar COPE don yin takara da Zuma, ya sa wasu kafofin watsa labarai na wurin suna ganin cewa, Jam'iyyar ANC sai ta yi da gaske in tana son samun babbar nasara bisa tushen babban zabe da aka yi a shekara ta 2004.
1 2 3
|