Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-20 21:06:19    
Gwamnatin kasar Sin ta taimaki kananan masana'antu wajen yin takarar matsalar kudi ta duniya

cri

B

isa wannan dalili ne, gwamnatin kasar Sin ta kebe wasu kudade domin tallafawa muhimman matsakaita da kananan masana'antun da suke da nasaba da zaman rayuwar jama'a. A nan gaba ba da dadewa ba, ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin za ta kebe kudaden da za su kai kudin Sin yuan biliyan 15 domin kyautata fasahohin yin kayayyaki na matsakaita da kananan masana'antu.

Mr. Li Yizhong, ya bayyana cewa, kara karfin kyautata fasahohin yin kayayyaki a matsakaita da kananan masana'antu ba ma kawai zai iya yin amfani ga kokarin tinkarar matsalar kudi ta duniya da bunkasa tattalin arziki ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne zai iya bayar da muhimmiyar gudummawa ga ayyukan daidaita sana'o'i da canja hanyar bunkasa tattalin arziki domin neman wata kyakkyawar makoma a nan gaba. Mr. Li Yizhong ya ce, "Yanzu farashin danyun kayayyaki da na injuna yana raguwa sosai a kasuwannin kasa da kasa. A lokacin da ake fama da tabarbarewar tattalin arziki, ya kamata a zuba kudi domin kyautata fasahohin yin kayayyaki. Bayan da aka kammala wannan aiki, za a iya samun ci gaba lokacin da tattalin arziki ya samu karuwa. Kuma za a iya fanshe dukkan kudaden da aka zuba cikin sauri."

Masana sun bayyana cewa, ba ma kawai gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da wasu kyawawan manufofi don matsakaita da kananan masana'antu musamman ba, har ma ta soma aiwatar da shirin zuba jarin da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan 4000 tun daga karshen shekara ta 2008. Matsakaita da kananan masana'antu sun kuma samu moriya sosai daga wannan shirin da ke da nasaba da zaman rayuwar jama'a da ayyukan da ba su samar da riba da ayyukan yau da kullum. Mr. Zhu Baoliang, masanin harkokin tattalin arziki da ke aiki a cibiyar nazarin bayanai ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Muna dukufa ka'in da na'in wajen habaka bukatu a kasuwannin cikin gida, kamar nuna goyon baya ga matsakaita da kananan masana'antu. Idan tattalin arziki ya sake samun karuwa a wata rana, matsakaita da kananan masana'antu za su iya samun ci gaba sakamakon karuwar tattalin arzikin manyan masana'antu da kamfanoni."

Kana kuma, ba ma kawai gwamnatin tsakiya ta kasar Sin tana taimakawa matsakaita da kananan masana'antu don kokarin fita daga mawuyacin hali ba, har ma gwamnatocin wurare na kasar suna kuma kokarin taimakawa matsakaita da kananan masana'antu. A kwanan baya, a bayyane ne gwamnatin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin ta tsai da kudurin samar da kudin Sin yuan biliyan 2.2 ga matsakaita da kananan masana'antu don su samu damar fita daga mawuyacin hali. Wasu 'yan kasuwa suna ganin cewa, matakin da gwamnatin lardin Guangdong ta dauka ya ba da hakikanin jagoranci mai amfani ga matsakaita da kananan masana'antu don tinkarar matsalar kudi ta duniya. Mr. Bao Jiejun wanda ke samar da kayayyakin fadi-ka-mutu ya bayyana cewa, "Gwamnati ta kebe kudin Sin yuan biliyan 2.2 domin nuna goyon baya ga matsakaita da kananan masana'antu, wannan wani hakikanin mataki ne. A ganina, wannan mataki zai ba da hakikanin jagoranci ga makomar duk lardinmu, ciki har da masana'antu."

A lokacin da ake kokarin tinkarar matsalar kudi ta duniya, matsakaita da kananan masana'antun kasar Sin suna kuma daidaita tsarin kayayyakinsu a kai a kai. Suna kokarin kara karfin kayayyakinsu na yin takara a kasuwa ta hanyoyin kyautata ingancin kayayyaki da kara fasahohin zamani wajen kera kayayyaki da kuma kara daraja ga kayayyakinsu.

Bugu da kari kuma, gwamnatin kasar Sin ta yi dimbin aiki wajen taimakawa matsakaita da kananan masana'antu domin raya sabbin kasuwanni a duniya. Alal misali, yanzu yawan kayayyakin da ake bukata a kasuwannin kasashen Turai da Amurka da kuma Japan yana ta raguwa. Gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin bude sabbin hanyoyin sayar da kayayyaki a kasuwannin kasashen Latin Amurka da na Gabas ta tsakiya. Sannan tana kokarin kafa shiyyoyin yin hadin gwiwa a fannonin cinikayya da tattalin arziki da su zama muhimman dandalin da matsakaita da kananan masana'antun kasar Sin za su iya sayar da kayayyakinsu. (Sanusi Chen)


1 2 3