Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-20 21:06:19    
Gwamnatin kasar Sin ta taimaki kananan masana'antu wajen yin takarar matsalar kudi ta duniya

cri

Yanzu an rage yawan kayayyakin da ake fitar da su daga kasar Sin zuwa kasuwannin duniya sakamakon matsalar kudi ta duniya. Saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya ragu. A gaban hali mai tsanani da ake ciki, wasu matsakaita da kananan masana'antun kasar Sin sun fada mawuyacin hali, har ma an rufe wasu daga cikinsu. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta bullo da jerin manufofin hada hadar kudi da kara kyautata fasahohi ga masana'antu matsakaita ko kanana domin sassauta mawuyacin halin da suke ciki.

Mr. Du Xiangqing, babban direkta ne na wani kamfanin kera injuna a birnin Chongqing. Kwanan baya, wani kamfanin kasar waje ya nuna sha'awa ga kayayyakin da kamfaninsa ke kerawa, kuma wannan kamfanin yana son bai wa Mr. Du kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan miliyan 20 domin yin odar kayayyakin kamfaninsa, amma Mr. Du ya nuna damuwa sakamakon rashin wani sashi na kudaden cika kwangila. Sabo da haka, kamfanin ba da lamuni na birnin Chongqing ya ba shi lamunin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu dari 4. Mr. Du ya bayyana cewa, "Kamfanin ba da lamuni ya nuna mana hakikanin goyon baya. Da ba mu samu tallafin kudin da kamfanin ba da lamuni ya ba mu ba, kamfaninmu ba zai iya komawa hanyar samun karuwa kamar yadda ake fata ba."

1 2 3