Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-20 21:06:19    
Gwamnatin kasar Sin ta taimaki kananan masana'antu wajen yin takarar matsalar kudi ta duniya

cri

Yawan GDP da irin wadannan matsakaita da kananan masana'antu suka samar ya kai kashi 60 cikin kashi dari bisa na jimillar GDP a kasar Sin, kuma suna samar da guraban aikin yi da yawansu ya kai kusan kashi 80 cikin kashi dari bisa na dukkan guraban aikin yi da ake samarwa a kasar. Amma bayan abkuwar matsalar kudi ta duniya, tun daga karshen rabin shekara ta 2008, matsakaita da kananan masana'antu sun fi fama da wahala wajen neman jari. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta sa kaimi ga hukumomin ba da lamuni da su taimaki irin wadannan masana'antu, kuma ta nemi bankunan da su samar musu karin rancen kudi.

Haka kuma, gwamnatin tsakiya da gwamnatocin matakai daban daban na kasar Sin sun rage harajin da ake bugawa kan matsakaita da kananan masana'antu domin rage nauyin da ke kansu. Alal misali, kasar Sin ta kara harajin kwastam da take mayar wa masana'antun saka har sau 4 domin nuna goyon baya ga matsakaita da kananan masana'antun saka da su fitar da kayayyakinsu da tufafi zuwa kasashen waje. Bugu da kari kuma, gwamnatin kasar Sin ta rage yawan haraji iri iri da ake bugawa kan masana'antu.

Kana kuma, gwamnatin kasar Sin ta samar da kudin musamman domin tallafawa matsakaita da kananan masana'antu da su kirkiro sabbin fasahohi da daidaita tsarin matsakaita da kananan masana'antu da kuma zamanintar da sana'o'in kasar. Bugu da kari kuma, gwamnatin kasar Sin ta sa kaimi ga matsakaita da kananan masana'antu da su kirkiro sabbin hanyoyin samar da kayayyaki domin kara karfin takara a kasuwa. Mr. Li Yizhong, ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin ya bayyana cewa, "Kyautata fasahohin yin kayayyaki hanya ce mafi sauki wajen bunkasa tattalin arziki da gudummawar da masana'antu suke bayarwa zaman al'umma ta hanyar zuba jari."

1 2 3