Amma Chen Si ba ta jin tsoro kamar yadda Sun Hao ke yi, inda ta ce,"A ganina, a duk lokacin da muke amfani da wannan fasaha, bai samu kwanciyar hankali ba. Ya kan ji tsoro na sake fadawa. Abin da ya faru a da ya tsorata shi sosai. Amma saboda abun ya faru cikin sauri, shi ya sa ban mayar da martani ko kadan ba."
A lokacin aikin horaswa, nagartacciyar fasahar Sun Hao ta yin rawa da kuma dimbin fasahohinsa sun taimakawa Chen Si sosai. A sa'i daya kuma, karfin zuciyar Chen Si da aiki tukuru da take yi ya burge wannan saurayi. Bayan aukuwar wannan hadarin keken guragu, Sun Hao ya nemi taimakawa Chen Si, amma Chen Si ta ki. Ta gaya masa cewa, "A'a, na iya." Wannan ya burge Sun Hao sosai. Ba tare da boye kome ba, Sun Hao ya ce, a farkon lokacin da yake yin mu'amala da masu yin rawa kan keken guragu, ya ji tausayinsu a zuciyarsa. A wancan lokaci, bai san cewa, tausayi na matsayin na abu na farko da nakasassu ba su bukata ba. A kwana a tashi, ya fahimci karfin zuciya irin na musamman da nakasassu suke mallaka. Sun Hao ya bayyana cewa,"A farkon lokacin da nake tuntubar masu yin rawa kan keken guragu, sai tausaynsu nake yi. Ina tausayi musu ne saboda su nakasassu ne. Amma su nakasassu su kan gaya mini cewa, suna da karfin zuciya. Sannu a hankali, mun mayar da su a matsayin tamkar wadanda suke kasancewa cikin koshin lafiya. Ta haka sun sami daidaituwa a zukatansu. Mai yiwuwa ne wannan shi ne abin da ya fi dacewa gare mu mutanen da muke da koshin lafiya da mu yi koyi a wajensu, wato samun karfin zuciya."
Aikin horaswa na yin rawa kan keken guragu har na tsawon watanni 3 ya sake haskaka ran Chen Si. Tare da nuna budaddiyar zuciya, wannan kyakkyawar budurwa ta ce, a cikin wadannan watanni 3 da suka wuce, ta kara imani, haka kuma, ta fi yin dariya. Dangane da makoma, abubuwan da ta fada cikin natsuwa sun nuna karfin zuciyarta da kuma babban burinta, inda ta ce, ba ita kadai ba ce, tana fatan za a iya shigar da karin nakasassu cikin wasannin raye-raye kan keken guragu. Chen Si ta ce,"Nan gaba, ina son in iya yin talla game da yin rawa kan keken guragu. A kasar Sin, wannan shi ne karo na farko da aka shirya gasar yin raye-raye kan keken guragu. Ina neman raya wasan raye-raye kan keken guragu zuwa sabon mataki. Ina kokarin ganin matsayin kasarmu na yin raye-raye kan keken guragu ya fi saura na kasashen duniya." 1 2 3
|