Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-20 09:46:46    
Yin rawa kan keken guragu ko kuma tare da guragun a kan kekensu

cri

Masu karatu, a kusa da mu, da akwai nakasassu da yawa da suke yin ayyuka kamar yadda muke yi, kuma suna jin dadin zaman rayuwa kamar yadda muke ji. Ba za a iya bambance mu da su ba, saboda dukkanmu daya ne.

A kwanan baya, a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin, tare da zuwan lokacin bazara, an yi budaddiyar gasar raye-raye kan keken guragu ta duniya. A yayin gasar, 'yan wasa fiye da 70 da suka zo daga kasashen Japan da Korea ta Kudu da Sin da sauran kasashe da yankuna 8 sun nuna wa 'yan kallon shagulgulan musamman na raye-raye kan keken guragu tare da nuna jaruntaka da karfin zuciya. Yau ma za mu gabatar muku da wani dan wasa da ke da koshin lafiya da wata 'yar wasa nakasasshiya da suka yi raye-raye kan keken guragu tare.

Raye-raye kan keken guragu sun girgiza mutane sosai, ciki har da wani nau'in raye-rayen da ke bukatar wani mai yin rawa kan keken guragu da kuma wani mai yin rawa da ke da koshin lafiya da su hada kai. Ko da yake masu yin rawa kan keken guragu sun nakasa a kofofinsu, amma sun kware sosai wajen yin amfani da keken guragu, kamar dai keken guragun ya kasance wani bangare ne na jikinsu. A sakamakon yin amfani da keken guragu, sun bayyana fahimtarsu da soyayyarsu kan raye-raye ta hanyar yin amfani da jikunansu da ke da koshin lafiya.

A yayin gasar, Chen Si da Sun Hao da suka zo daga lardin Shanxi na kasar Sin sun zama na uku a yayin gasar raye-raye irin na Latin Amurka. Wannan shi ne maki mafi kyau da 'yan wasan kasar Sin suka samu a cikin wannan gasa. Chen Si mai shekaru 22 da haihuwa wata budurwa ce mai kyan gani. Ta fara koyon raye-rayen gargajiya tun bayan da shekarunta suka kai 5 da haihuwa. Tana kishin dukkan abubuwan da suka shafi raye-raye matuka. Amma duk da haka, a yayin da shekarunta suka kai 12 da haihuwa, wani hadarin mota ya yi sanadiyyar rasa dukkan kafofinta. Wannan budurwa ba ta iya jure bakin cikin rasa kofofinta duka cikin gajeren lokaci ba. A wancan lokaci, raye-raye sun kaura a zuciyarta. Ta gaya mana cewa,"Bayan aukuwar hadarin mota, ba na son a ambaci raye-raye. Mahaifiyata ta yayyaga dukkan bayanai da hotuna da takardun yabo da na samu a da da sauran abubuwan da suka shafar raye-raye."

1 2 3