Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-20 09:46:46    
Yin rawa kan keken guragu ko kuma tare da guragun a kan kekensu

cri

Ko da yake wata budurwa ba ta ambaci raye-raye ba, amma a zuciyarta, ba za ta taba mantawa da raye-raye ba. A watan Disamba na shekara ta 2008, cibiyar kula da wasannin Olympic na nakasassu ta kasar Sin ta je lardin Shanxi domin daukar 'yan wasan raye-raye kan keken guragu. Wannan ya kyautata zaman rayuwar Chen Si, wanda bai sauya ba har na tsawon shekaru 10. Ya kuma haskaka zuciyar wannan budurwa. Bayan kara fahimtar halin da Chen Si take ciki, cibiyar ta karbe ta dan shiga raye-raye kan keken guragu. Chen Si ta sifanta mana yadda ta yi farin ciki a wancan lokaci, inda ta ce,"Na yi matukar farin ciki saboda ina iya yin raye-raye kan keken guragu. A ganina, ina kasancewa tamkar cikin mafarki. A yayin da nake karama, ina son raye-raye sosai. Amma bayan aukuwar hadarin mota, ina tsammani cewa, zan yi da-na-sani a duk tsawon raina. Ban iya ci gaba da raye-raye ba. Bayan watan Disamba na shekarar bara, na soma yin rawa kan keken guragu. Ina farin ciki kwarai. Kome zai yi kyau a gare ni, muddin na iya yin rawa."

Tare da zumudin sake yin rawa, Chen Si ta kama hanyar koyon yin rawa kan keken guragu. A cikin 'yan watanni 3 ko fiye da suka wuce, Chen Si ta sami saurin ci gaba, a sakamakon harsashin da ta dasa a lokacin da take karama da kuma taimakon da abokin rawarta Sun Hao yake ba ta.

Sun Hao mai shekaru 26 da haihuwa da yake da koshin lafiya ya yi shekaru 15 yana yin raye-rayen wasannin motsa jiki. Shi ma wani dan wasan raye-raye ne. Bullowarsa ta tuna wa Chen Si da abubuwa game da raye-raye da ba ta ambata ba har na tsawon shekaru da dama, sa'an nan kuma, ta kawo mata fasahar yin rawa cikin sauri. Ko da yake Sun Hao ya kware ne wajen yin rawa, amma tun daga karshen shekarar bara, ya fara samun fahimta dangane da raye-raye kan keken guragu. Shi ma ya fara koyon irin wanann rawa tun daga farko. Wadannan samari biyu sun fara koyon sabuwar rawa tare sannu a hankali. A cikin aikin horaswa da suka yi a wani karo, Sun Hao ba shi da wata fasaha sosai, shi ya sa har ma Chen Si ta fadi tare da keken guragunta. Wannan ya tsorata Sun Hao kwarai da gaske. Daga baya, a duk lokacin da suke amfani da wannan fasaha, Sun Hao kan mara wa Chen Si baya domin hana ta fadawa. Sun Hao ya gaya mana cewa, har zuwa yanzu bai iya jure tsoron da wannan fasaha ta kawo masa ba. Yana mai cewar,"Har zuwa yanzu, ina tsoron yin amfani da wannan fasaha."

1 2 3