A yayin taron NPC da aka shirya a shekara ta 2006, Maliya Mati ta samu wata dama mai daraja sosai wajen yin hira tare da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao. Lokacin da ta tuna da wannan batu, Maliya Mati ta yi farin ciki kwarai, kuma ta gaya mana cewa, ran 8 ga watan Maris na shekara ta 2006, rana ce ta bikin mata na duniya. Firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya halarci taron kungiyar wakilai ta jihar Xinjiang, don sauraren ra'ayoyi. Bayan da wakilai fiye da goma suka yi jawabi, Wen Jiabao ya ba da wata shawara, wato bayar da damar yin jawabi ta karshe ga wani wakili ko wakiliya daga kananan hukumomi. Bayan da ya ga sunan Maliya Mati da ta fito daga kauye a takardar sunayen wakilan, ya ce, "Bari mu ji ra'ayi na Maliya Mati." Sabo da haka, Maliya Mati ta samu damar gabatar da wata shawara ga Wen Jiabao, ta cewar ko kasar Sin za ta iya gudanar da harkokin ba da tabbaci ga matsayin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyuka kamar yadda ake yi a birane? Wen Jiabao ya karbi shawarar da ta bayar, kuma ya shigar da ita cikin rahoton ayyuka na gwamnati a shekara ta 2007, inda ya rubuta cewa, za a kafa tsarin tabbatar da matsayin zaman rayuwa mafi kankanta na kauyuka a duk kasar Sin.
Sabo da haka, garin Maliya Mati ya kasance wuri na farko da kasar Sin ke gudanar da tsarin tabbatar da matsayin zaman rayuwa mafi kankanta na kauyuka. Yanzu, ana gudanar da tsarin a yankunan da ke yamma maso tsakiyar kasar Sin a dukkan fannoni.
Maso sauraro, waka mai dadin ji da kuke saurara yanzu wata waka ce ta kabilar Kirgiz, wadda ake kiranta "Flanton Pamirs". Kuma muna fatan Maliya Mati da ta zo daga flanton Pamirs za ta iya bayar da shawarwarin da ka iya amfanawa jama'a a yayin taron NPC na shekarar bana.(Kande Gao) 1 2 3
|