Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-09 21:46:06    
Musulmai 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC

cri

Sabo da haka a yayin taron NPC da aka kira a shekarar da ta gabata, Ma Hanlan ta yi kira da a shigar da gundumar Dongxiang cikin gundumomi masu fama da talauci mai tsanani, da kuma kara karfin tallafawa gundamar domin fitar da ita daga mawuyacin hali.

Yanzu shekara guda ta wuce, Ko Ma Hanlan za ta bayar da sabbin shawarwari a kan bunkasuwar gundumar a gun taro na shekarar da muke ciki? A yayin taron NPC mai zuwa, zan yi hira tare da Ma Hanlan, kuma a cikin shirye-shriyenmu masu zuwa, zan ci gaba da gabatar muku da labarinta. To yanzu bari mu saurari wata waka ta kabilar Dongxiang, wadda ake kiranta "Kyakkyawar gundumar Dongxiang garinmu ne".

Yanzu zan gabatar muku da wata musulma 'yar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta daban da ta zo daga kabilar Kirgiz ta jihar Xinjiang da ke arawa maso yammacin kasar Sin, wadda ake kiranta Maliya Mati.

Maliya Mati, wata 'yar majalisar NPC ce daga flanton Pamirs. A cikin 'yan majalisar a karo na 11 da yawansu ya kai 2987, garin Maliya Mati ya fi zama nesa da birnin Beijing. Maliya Mati ta fito ne daga gundumar Kezilesu mai cin gashin kai ta jihar Xinjiang, ita ce kuma 'yar majalisar daya tak daga kabilar Kirgiz a nan kasar Sin.

Kabilar Kirgiz tana daya daga cikin kananan kabilu guda goma masu bin addinin Musulunci na kasar Sin, yawancinsu suna zaune ne a flanton Pamirs, yawan 'yan kabilar ya kai sama da dubu 160. Bisa dokar zabe da abin ya shafa ta kasar Sin, ana iya zabar 'dan majalisar ko 'yar majalisar guda daya daga kabilar Kirgiz. Abin farin ciki shi ne Maliya Mati mai shekaru 38 da haihuwa ta zama wannan 'yar majalisar daya tak.

Ko da yake shekarun Maliya Mati da haihuwa ba su da yawa, amma ta riga ta kasance 'yar majalisar har shekaru da dama. A shekara ta 2003, Maliya Mati ta zama wata 'yar majalisar NPC a karo na 10. A wancan lokaci kuma ita ce wata jami'a ta yau da kullum da ke aiki a kananan hukumomi a kauyuka na gundumar Kirgiz.

1 2 3