Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-09 21:46:06    
Musulmai 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC

cri

A mako mai zuwa wato daga ran 5 ga watan Maris, za a kira taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato NPC, wadda kuma ta kasance hukumar koli da ke gudanar da harkokin mulkin kasar Sin. Taron dai wani muhimmin al'amari ne na harkokin siyasa na jama'ar kasar Sin, wanda zai tsai da burin da Sin take son cimmawa cikin sabuwar shekara a fannin bunkasuwa, kuma zai yi bincike a kan daftarin dokokin da ke shafar zaman rayuwar jama'a da kuma kada kuri'a a kansu. A cikin taron kuma, ana iya samun musulmai 'yan majalisar NPC kusan dari daya, wadanda suke bayar da gudummowa sosai wajen raya kasar. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wasu musulmai 'yan majalisar.

A kasar Sin, ana iya samun musulmai a cikin kabilu 10, wato kabilun Hui da Uygur da Kazak da Tatar da Tajik da Uzbek da Kirgiz da Dongxiang da Sala da kuma Bao'an. Dukkan wadannan kabilu suna da wakilansu da ke halartar taron NPC domin kula da hakkinsu na tsai da kudurin raya kasar Sin. Da farko, zan gabatar muku da wata musulma 'yar majalisar da ta zo daga kabilar Dongxiang, wadda ake kiranta Ma Hanlan.

An haifi Ma Hanlan a gundumar Dongxiang ta kasar Sin, kuma ta yi girma ne a wannan wuri. Da farko ta taba gudanar da aikin kula da yin haihuwa bisa tsari, a shekara ta 2006 kuma ta shiga hukumar yawon shakatawa ta gundumar Dongxiang. Haka kuma a shekara ta 2008, ta zama wata 'yar majalisar wakilan jama'ar Sin ta hanyar zabe, haka kuma ita ce 'yar majalisa daya tak a jihar Gansu ta kasar Sin a fannin yawon shakatawa. Ma Hanlan ta gaya mana cewa, ta lura da wannan dama sosai da ta sa ta zuwa Beijing don halartar wannan gagarumin taro na kasar Sin a madadin dukkan 'yan kabiar Dongxiang.

Ban da wannan kuma, a matsayinta na wata tsantsar 'yar kabilar Dongxiang, Ma Hanlan mai shekaru 27 da haihuwa ta fahimci garinta sosai. Ta bayyana cewa, gundumar kabilar Dongxiang mai cin gashin kai gunduma ce daya tak a duk fadin kasar Sin da ake iya samun dimbin 'yan kabilar Dongxiang a ciki, kuma take iya gudanar da harkoki da kanta, haka kuma tana daya daga cikin gundumomin kananan kabilu da suke fama da talauci mai tsanani a kasar. Gundumar kabilar Dongxiang tana da mutane dubu 271.3, a ciki yawan 'yan kabilar Dongxiang ya kai kashi 84.19 cikin kashi dari. Yayanin halitta na wurin ba kyau sam, ko da yaushe a kan yi fama da bala'in fari.

1 2 3