|

Mr. Juma Mwapachu, babban sakataren kungiyar raya kasashen gabashin Afirka ya bayyana cewa, kara yin hadin gwiwa a tsakanin kungiyoyin shiyya-shiyya da yin amfani da makamashin halittu tare hanya kadai da za a iya bi domin kara karfin takara na kasashen Afirka a duniya. Idan ba za a iya canja halin koma baya da ake ciki a Afirka a fannin ayyukan yau da kullum ba, to, za a bace damar raya tattalin arziki da kasashen Afirka suka samu bayan da suka dade suna kokarin samunta.
Bisa shirin da aka tsara, wannan "hanyar bunkasa tattalin arziki da za ta hada arewa da kudancin Afirka" za ta tashi daga tashar ruwa ta Dares Salam na kasar Tanzania zuwa tashar ruwa ta Durban ta kasar Afirka ta kudu. (Sanusi Chen) 1 2 3
|