
Mr. Mwencha, mataimakin shugaban kwamitin kungiyar AU ya nuna cewa, samar da ayyukan yau da kullum masu inganci muhimmiyar hanya ce wajen kara karfin takara na tattalin arzikin Afirka. Amma yanzu ayyukan yau da kullum na yawancin kasashen Afirka da muhallin zirga-zirga da sufuri na Afirka suna matsayin koma baya sosai. Suna kuma dakatar da ci gaban tattalin arzikin Afirka.
Sabo da haka, Mr. Mwencha ya yi kira ga kasashen Afirka da su kara saurin zuba jari kan tagwayen hanyoyin mota da tasoshin ruwa da hanyoyin dogo da hanyoyin jiragen sama da sadarwa da ayyukan samar da wutar lantarki da sauran ayyukan yau da kullum domin dacewa da shirin kafa "hanyar bunkasa tattalin arziki da za ta hada arewa da kudancin Afirka" da kuma kara yin hadin gwiwa da mu'ammala a tsakanin shiyya-shiyya.
Mr. Pascal Lami, babban direktan kungiyar cinikayya ta kasa da kasa, wato WTO ya kuma bayyana cewa, shirin kafa "hanyar bunkasa tattalin arziki da za ta hada arewa da kudancin Afirka" yana da muhimmanci sosai ga kokarin bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka. Raya ayyukan yau da kullum hanya ce mafi dacewa ga kasashen Afirka wajen yin amfani da tallafin kudin da sauran kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa suke samar musu.
1 2 3
|