Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-09 20:52:53    
Afirka: shirin kafa "hanyar da ke sada arewa da kudancin kasashen Afirka"

cri

A ran 7 ga wata a birnin Lusaka na kasar Zambia, kungiyoyin shiyya-shiyya uku, wato kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen kudancin Afirka bai daya, wato SADC da kungiyar bunkasa kasashen da ke kudu maso gabashin Afirka, wato COMESA da kungiyar bunkasa kasashen gabashin Afirka bai daya, wato EAC sun bayar da wata sanarwa cikin hadin gwiwa, inda suka sanar da cewa, za su yi amfani da shekaru 5 zuwa shekaru 10 masu zuwa wajen kafa wata "hanyar bunkasa tattalin arziki da za ta hada arewa da kudancin kasashen Afirka". Bisa shirin da aka tsara, suna fatan za a iya kafa wata hanyar zirga-zirga da ke iya rage kudaden sufurin kayayyaki da samun karin moriyar tattalin arziki da kuma samar da kyawawan ayyukan yau da kullum.

A ran 6 ga wata, shugabannin kasashen Zambia da Kenya da Uganda da Afirka ta kudu da wasu manyan jami'an kungiyoyin kasa da kasa sun yi amfani da kwanaki 2 sun yi taro a birnin Lusaka na kasar Zambia, inda suka samu nasarar shawo kan bankin duniya da kungiyar cinikayya ta kasa da kasa, wato WTO da kungiyar kawancen kasashen Turai, wato EU da kuma bankin raya Afirka, wato ADB sun rattaba hannu kan shirin samar da dalar Amurka biliyan 1.2 ga wannan shiri. Bugu da kari kuma, kasashen Sin da Japan da Amurka da bankin zuba jari na Turai sun kuma bayyana sha'awarsu kan wannan shiri.

Wannan sanarwa ta bayyana cewa, kungiyoyin shiyya-shiyya uku na Afirka sun riga sun samu ra'ayin bai daya, suna ganin cewa, "hanyar bunkasa tattalin arzikin Afirka da za ta hada arewa da kudancin Afirka" wani muhimmin aiki ne da ke bunkasa tattalin arzikin shiyya-shiyya na Afirka. Ba ma kawai wannan hanya za ta sa kasashen Afirka su yi amfani da makamashinsu ba, har ma za ta iya jawo karin masu zuba jari na duniya da su je kasashen Afirka.

1 2 3