Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-09 14:13:03    
Jihar Guangxi ta raya aikin gona na musamman domin neman arziki a kauyuka

cri

Ba ma kawai mangwaron da aka noma a gundumar Tianyang a lokacin sanyi ya canja tarihi, wato a kan noma mangwanro a lokacin zafi ba, hatta ma ya wadata kasuwar 'ya'yan itatuwa a yankunan arewacin kasar Sin, har ma a wasu kasashen da ke kudu maso gabashin Asiya.

Sabo da ana sayar da mangwaro a kasuwa kamar yadda ake fata, manoman da suke noman mangwaro na gundumar Tianyang sun kuma samu arziki. Mr. Huang Xiaoning, shugaban gundumar Tianyang ya ce, a da, mangwaron da manoman wurin suke nomawa iri daya ne kadai, kuma ba su iya noman shi sosai ba. Kuma ba su iya samun bayanai daga kasuwa ba. Sakamakon haka, manoman wurin sun saba da zaman rayuwa na fama da talauci a kullum. Yanzu, wannan unguwar kimiyya da fasaha ta raya aikin gona ta sa manoman wurin sun samu sabbin fasahohi da sabbin ire-iren mangwaro, kuma sun samu arziki. Mr. Huang ya ce, "Ana amfani da sabbin ire-iren mangwaro da aka shigo da su a unguwar kimiyya da fasaha ta raya aikin gona a gonakin gundumarmu. Sabo da haka, suna amfana wa kokarin kyautata ingancin amfanin gona da kara yawan amfanin gona da muke samu da moriyar aikin gona baki daya."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, raya aikin gona bisa ma'aunin da ake bi, da kuma raya tambarin amfanin gona a kasuwa sun zama muhimmin burin da jihar Guangxi ke neman cimmawa domin raya aikin gona a lokacin sanyi, kuma a lokacin kaka a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta. Jihar Guangxi ta riga ta zama daya daga cikin sansanonin noman amfanin gona a lokacin da ba a saba noma ba a kasar Sin. A shekarar da ta gabata, yawan kudaden da jihar Guangxi ta samu daga aikin gona na lokacin sanyi ya riga ya kai kudin Sin yuan biliyan 20. Yawan karin kudaden shiga da kowane manomin jihar ya samu ya kai kudin Sin yuan dari 3. Yanzu ana noman amfanin gona a lokacin sanyi a duk fadin jihar Guangxi, yawan gonaki ya kai kusan hekta miliyan 1.

Yanzu, gwamnatocin matakai daban daban na jihar Guangxi suna kokarin raya aikin gona irin na musamman a duk fadin jihar domin kyautata tsarin sana'o'in aikin gona da kara yawan kudin shiga da manoma ke samu da kyautata zaman rayuwarsu. (Sanusi Chen)


1 2 3