Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-09 14:13:03    
Jihar Guangxi ta raya aikin gona na musamman domin neman arziki a kauyuka

cri

Kamar yadda manoman kauyen Bainiu suke yi, manoman kauyen Zhongping na birnin Baise sun kuma samu arziki bayan da suka soma noman lawashi mai dadin ci. Lokacin da ake zantawa kan wannan lawashi mai dadin ci, tabbas ne a ambaci Liu Yuyan, mai shekaru 53 da haihuwa wadda ta kware sosai wajen noman lawashi mai dadin ci. Ta fi sauran manoman wannan kauye samun arziki sabo da ta kan shuka lawashi mai dadin ci. Ba ma kawai ta shuka lawashi mai dadin ci da kanta ba, hatta ma ta kafa wata kungiyar 'yan amshi domin yada ilmin noman lawashi mai dadin ci ga sauran manoma ta hanyar rera wakoki. Mijinta ya taimake ta wajen rubuta kalmomin wakokin yada ilmin noman lawashi mai dadin ci.

"Kauyen Zhongping wuri ne da ke kawo albarka. Ya yi suna sabo da ana noman lawashi mai dadin ci. Ana sufurinsu zuwa duk kasar Sin, kuma ana ta yada labaru game da yadda manoman kauyen Zhongping suke noman lawashi mai dadin ci."

Yanzu, dimbin manoman kauyen Zhongping sun riga sun mallaki fasahar noman lawashi mai dadin ci. Yawan iyalan da suke samun kudin shiga fiye da kudin Sin yuan dubu 10 a kowace shekara ta fannin noman lawashi mai dadin ci ya wuce dari 3. Wasu daga cikinsu sun riga sun yi amfani da kudaden da suka samu domin gina gidajensu masu hawa 2 ko 3, wasu sun kuma sayi motoci.

Masana suna ganin cewa, jihar Guangxi tana da kyawawan sharuda wajen raya aikin gona irin na musamman bisa hakikanin halin da jihar ke ciki. Yankunan jihar Guangxi da suka kai kashi 40 cikin kashi dari na duk fadin jihar suna cikin yankunan yanayin zafi. Sakamakon haka, ana da isashen hasken rana da wadataccen albarkar ruwa. A duk shekara, ana iya noman amfanin gona iri iri, musamman ana iya noman kayayyakin lambu lokacin da ake cikin lokacin sanyi. Gwamnatin kasar Sin ta kafa wata unguwar kimiyya da fasaha ta raya aikin gona a gundumar Tianyang ta birnin Baise na jihar Guangxi domin sa kaimi wajen raya aikin gona irin na musamman. Yanzu gundumar Tianyang tana amfani da kyawawan sharudan da aka samar a cikin wannan unguwar kimiyya da fasaha ta raya aikin gona domin noman mangwaro. A karkashin taimakawar masana, manoman wurin suna noman mangwaro a lokacin sanyi. Mr. Zhong Hengqin, jami'in gundumar Tianyang ya bayyana cewa, "Mu kan shirya kwas ga manoma kan yadda za a iya noman mangwaro a lokacin sanyi. Muna gayyato shehunan malamai wadanda suka yi suna wajen noman mangwaro domin koyar da ilmin noman mangwaro. A waje daya, mun kafa wata kungiyar sayar da mangwaro a duk kasar Sin ta yadda manoma za su iya samun wani kyakkyawan farashi a kasuwa."

1 2 3