Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-09 14:13:03    
Jihar Guangxi ta raya aikin gona na musamman domin neman arziki a kauyuka

cri

Jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta jiha ce mafi girma da ke kunshe da kananan kabilu da yawa. Galibin wadannan mutanen kabilu manoma ne. Ko da yake suna kokari sosai ta hanyoyi iri daban daban, amma ba a iya canja halin da suke ciki ba wajen fama da talauci cikin daruruwan shekarun da suka gabata sakamakon rashin isassun gonaki a yankunan tsaunukan da suke zaune. Amma a cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, zaman rayuwar manoman wurin yana samun sauye-sauye a kai a kai. Manoman jihar Guangxi suna raya aikin gona irin na musamman bisa halin da suke ciki a yankunansu a karkashin jagorancin gwamnatin wurin. Mr. Tang Wanqi, wani manomi ne na jihar Guangxi ya ce, "Kafin mu soma raya sana'ar aikin gona irin ta musamman a shekarar 1996, matsakaicin yawan kudin shiga na kowane manomin kauyenmu 'yan daruruwan yuan kudin Sin ne kadai. Amma bayan da muka soma raya sana'ar aikin gona irin na musamman, yawan kudin shiga da muke samu yana ta karuwa a kai a kai, wato ya zuwa shekara ta 2005, wannan adadi ya riga ya kai kudin Sin yuan dubu 5. Kuma a shekara ta 2007, matsakaicin kudin shiga da kowanenmu ya samu ya kai kudin Sin yuan dubu 8. Tabbas ne wannan adadi zai kai kudin Sin yuan dubu 10 a shekara ta 2008."

Mr. Tang Wanqi, wani dan kabilar Yao ne da ke zaune a kauyen Bainiu na birnin Hezhou. A da, manoman wurin sun dogara kan wasu gonaki da wasu shanu wajen neman kudin shiga, matsakaicin kudin shiga da kowane manomin kauyen ya samu bai kai kudin Sin yuan dari 4 ba a kowace shekara. Yau da shekaru 12 da suka gabata, Mr. Tang Wanqi, dakacin kauyen Bainiu wanda yake son ganin kubutar manoman kauyensa daga talauci a kullum, kuma ya taba koyon fasahohi da ilmi a sauran wuraren kasar Sin ya koma kauyensa kuma ya koma da ilmi da fasahohin fama da talauci. Bisa shawararsa, kuma a karkashin jagorancinsa, manoman wurin sun hade dukkan gonaki tare sun soma shuka itatuwan lemo. Kuma kauyen Bainiu ya samu nasara. Ya zuwa shekara ta 2007, yawan gonakin da aka shuka itatuwan lemo ya kai fiye da hekta 140 a kauyen Bainiu. Sakamakon haka, yawan kudin shiga da manoman kauyen suke samu ya samu karuwa sosai. Lokacin da yake zantawa kan zaman rayuwa na yanzu, manomi Tang Wangfu na kauyen Bainiu ya nuna farin ciki sosai ya ce, "Yanzu kusan dukkan mazauna kauyenmu suna da na'urorin lantarki na gida, kamar su na'urar kashe kwayoyin cututtuka da akwatin sanyi da babur."

1 2 3