Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-08 13:57:28    
Ya zama wajibe kasashe daban-daban su hada kansu wajen murkushe 'yan fashin tekun Somaliya

cri

Sanin kowa ne ake ta yin rikicin yake-yake a cikin fadin kasar Somaliya tun daga shekarar 1991. a yanzu haka dai, yawancin wuraren kasar Somaliya na cikin halin kara-zube ; kuma gwamnatin kasar ta gaza maido da yanayin tsaro na cikin kasar daidai bisa hasashen da wassu kasashen ketare suke yi, balle yin dabaibayi kan 'yan fashin tekun., wadanda suke da alaka da dakarun kabilun kasar. Ban da wadannan kuma jama'ar kasar ta Somaliya suna fama da talauci saboda adadin kudin da kowanensu ya kan samu daga aikin kawo albarka wato GDP a kowace shekara ya yi kasa da dalar Amurka 800 kawai. Saboda haka, aika-aikan fashin teku ka iya tabbatar da samun bunkasar rayuwa sakamakon makudan kudaden fansa da 'yan fashi sukan samu. Game da wannan dai, kwararre Zhang Zhaozhong ya fadi cewa : ' Da farko dai, mahukantan gwamnatin Somaliya sun gagara gudanar da harkokin kasar yadda ya kamata. Saboda haka ne, babu tambanci tsakanin masu laifuffuka da wadanda ba su aikata laifi ba domin babu dokokin shari'a a wannan kasa. Sakamakon haka, rundunar sojin kasar ba ta da karfin tsaron haddin ruwanta da kuma yankunan tattalin arziki na musamman na tekun kasar. Ya kamata gamayyar kasa da kasa su kara tura sojoji masu kiyaye zaman lafiya zuwa wannan kasa don farfado da odar kasar yayin da suke tallafa mata da kuma shimfida demokuradiyya a wannan kasa'. ( Sani Wang )


1 2 3