Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-08 13:57:28    
Ya zama wajibe kasashe daban-daban su hada kansu wajen murkushe 'yan fashin tekun Somaliya

cri

'Yan fashin tekun Somalliya sun yi awon gaba da jiragen ruwa biyar na kasashen Jamus, da Yeman, da Faransa da kuma Burtaniya da kuma na yankin Taiwan na kasar Sin a 'yan kwanan baya a jere. Lamarin na nuna cewa 'yan fashin suna neman sake kunno kai. To, mene ne muhimman dalilan da suka sa yin haka ? Wani shahararren kwararre a fannon soja daga Jami'ar koyon ilmin soji ta kasar Sin, Zhang Zhaozhong ya fada wa wakilinmu cewa : ' Su 'yan fashin tekun Somaliya sun san muhallin mashigin tekun Aden da tekun India da kuma na haddin ruwa dake kewayen mashigin tekun Aden,har da yanayin sama na wadannan wurare da muhimman hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa da akan bi'.

Tun daga farkon wannan shekara, kungiyar tarayyar Turai wato EU da kasashen Amurka, da Sin da India da kuma sauran kungiyoyin kasashen duniya sun aike da wasu jiragen ruwan yaki zuwa mashigin tekun Aden dake arewacin Somaliya domin bada kariya ga jiragen ruwa. Saboda haka, yawan matsalolin fashin jiragen ruwa da ake yi a wannan haddin ruwa ya ragu bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Amma a cikin kwanaki biyu na baya, aika-aikan fashin jiragen ruwa sun karu ba zato ba tsammani, wadanda ga alama suke canjawa zuwa kudancin tekun India. Game da wannan dai, Mr. Zhang Zhaozhong ya furta cewa : ' Lallai 'yan fashin tekun Somalliya sun dan ji tsaro bayan da sojojin ruwa na kasashe daban-daban suka je wurin, inda suka fafata da 'yan fashin cikin dogon lokaci. Amma, sannu a hankali ne 'yan fashin suka takaita fasahohin da sukan samu har sun samu wassu dabarun tinkarar sojoji masu yin adawa da su'.

1 2 3