
Bisa la'akari da halin da ake ciki yanzu, 'yan fashin tekun Somaliya suna yadada aika-aikansu zuwa kudancin tekun Somalliya har zuwa wurin dake kusa da Zirin tekun Mozambique a kudu masu gabashin Nahiyar Afrika da zummar kaucewa jiragen ruwan yaki masu yin sintiri na kasashe daban-daban. Ko da yake sojojin ruwa na kasashe daban-daban sun tsaurara matakin bada kariya a haddin ruwa dake kusa da Somaliya, amma 'yan fashin ba su dakatar da aika-aikansu ba. Mr. Zhang Zhaozhong ya jaddada cewa, bisa halin da ake ciki yanzu, kamata ya yi kasashe daban-daban su hada kansu wajen yaki yayin da suke kara musayar bayanai. Yana mai cewa, wajibi ne kasashe daban-daban su yi musayar bayanai wa juna, ta yadda za a dauki matakai na bai daya don gudanar da yaki maimakon bada jaroganci da bangarori da dama suke yi.
1 2 3
|