Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-07 21:53:15    
An yi girgizar kasa mai tsanani a tsakiyar kasar Italiya

cri


Idan an duba tarihin kasar Italiya za a fahimci cewa, sau tari a kan samu girgizar kasa a kasar. A shekarar 1783, girgizar kasa a Calabria ta haddasa rasa rayukan mutane fiye da dubu 30. A shekarar 1915 kuma, mutane dubu 30 sun mutu sakamakon girgizar kasar da aka samu a Marsica wadda ita ma ta kasance a yankin Abruzzo. Sa'an nan a shekarar 1980, girgizar kasar da aka samu a Irpinia ta haddasa rasa rayukan mutane 2734. Bayan aukuwar girgizar kasa a ranar 6 ga watan Afrilu, wasu mutanen kasar Italiya sun yi korafe-korafe kan cewar masu binciken sanadin abkuwar girgizar kasa ba su aiwatar da aikinsu yadda ya kamata ba. Dagane da haka, wani jami'in kasar Italiya ya ce, girgizar kasar ta ranar 6 ga wata ta kasance bala'I mafi muni da ya ritsa da Italiya cikin karnin nan, ba zai yiwu ba wani ya iya yin hasashe kan lamarin.(Bello Wang)


1 2 3