
A halin yanzu mutanen duniya na mai da hankalinsu kan girgizar kasa mai tsanani da aka samu a tsakiyar kasar Italiya, da sanyin safiyar ranar 6 ga watan Afrilu, inda girgizar mai karfin awo 5.8 bisa ma'aunin Richter ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane a kalla 179, zuwa ranar 7 ga wata. Sa'an nan bisa halin da ake ciki, Silvio Berlusconi,firayin ministan kasar Italiya ya sanar da shimfida dokar ta-baci a kasar, don neman aiwatar da aikin ceto da kyau.
Yankin Abruzzo da girgizar kasa ta ritsa da shi ya kansace a tsakiyar kasar Italiya, inda ake samun tsaunuka da yawa, haka kuma an ce ana yawan samun girgizar kasa a yankin, kamar dai a ranar 29 ga watan da ya gabata, an yi wata girgizar kasa maras karfi a yankin. Sa'an nan girgizar kasa ta ranar 6 ga wata ta yi sanadiyyar hasara a garuruwa 26 na yankin Abruzzo. Kafofin watsa labaru na kasar Italiya sun ba da labarin cewa, zuwa sanyin safiyar ranar 7 ga watan Afrilu, mutane a kalla 150 sun mutu, sauran fiye da 1500 sun ji rauni, sakamakon girgizar kasar. Haka kuma jimillar da wakilinmu ya ruwaito da dumi-duminta ita ce, zuwa ranar 7 ga wata, girgizar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 179, kuma wasu 34 sun bace. Sai dai jimillar ba ta karshe ce ba, wato ana iya samun karuwa a kwanaki masu zuwa. Sa'an nan, ma'aikatan gwamnatin kasar Italiya sun ce girgizar kasa ta haddasa lahani ga iyalai fiye da dubu 40, kuma ta haddasa rugujewar gine-gine fiye da dubu goma, wadanda suka hada da mujami'a, da gidajen jama'a. Sauran hanyoyin mota da bututu mai samar da ruwa da yawa sun lalace sosai.
1 2 3
|