
A halin yanzu, sojojin kasar Italiya ,da 'yan sandan kasar masu kula da gandun daji,da ma'aikatan kashe gobara sun riga sun shiga aikin ceto. A ranar 6 ga wata da yamma, Silvio Berlusconi,firayin ministan kasar, ya kira taron manema labaru a wurin da bala'in ya shafa, inda ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta tura masu aikin ceto 5000 zuwa wurin, inda suka kafa tantuna 2500 a matsayin mafaka. Mazauna wurin da bala'in ya ritsa da su su ma sun kama aikin neman kubutar da wadanda suka raunata. Bayan abkuwar girgizar kasa, gwamnatin kasar Italiya ta ba da umurnin dakatar da daukar darussa a makarantu, da rufe tagwan hanya, haka kuma an yi la'akari da hanyar da za a bi don kaurar da mazauna wurin da bala'in ya shafa. Masu aikin sa kai na kasar Italiya sun tashi zuwa yankin Abruzzo don ba da nasu taimako a fannin kubutar da mutane. Kasashen Amurka, da Rasha, da Faransa, da Potugal, da Jamus da dai sauransu, sun nuna tausayawa ga mutanen da bala'in ya ritsa da su, wasunsu sun ce za su samar da tallafi.
1 2 3
|