
Kan dangantaka dake tsakanin Turai da Amurka, Mr Shi Yinghong ya bayyana cewa " dangantakar dake tsakanin Nahiyar Turai da Amurka ta danganta da yanayin tattalin arzikin duniya . tattalin arziki na da muhimmancin gaske ga ci gaban huldar dake tsakaninsu.idan tabarbarewa tattalin arziki ta kara tsanani,sabanin dake tsakaninsu ma zai kara yin muni, idan tattalin arzikin duniya zai farfado har sabon tsarin kudi ya shimfidu,to banbancin dake tsakaninsu zai ragu. Ga shi a halin yanzu muhimmin abu shi ne tattalin arzikin duniya yana cikin halin rashin sanin tabbas." (Ali) 1 2 3
|