Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-06 14:28:06    
Dangantakar da ke tsakanin Amurka da nahiyar Turai ta shiga yanayin rashin tabbas saboda rikicin kudi

cri

Wani muhimmin batun da aka tattauna a gun taron koli shi ne ta yaya za a inganta da kyautata dangantaka dake tsakanin nahiyar Turai da Amurka. Da akwai banbancin ra'ayi tsakanin Turai da Amurka saboda tsohuwar gwamnatin Amurka ta Bush ta bi manufarta ta kanta kan batutuwa da dama ciki har da batun Iraq.Tun lokacin da Barack Obakama ya hau karagar mulki ta Amurka manufar gwamnatin Amurka kan Turai ta yi dan sauyi mai amfani,ta kara jaddada muhimmancin hadin kan Turai da Amurka,ta kuma amince da muhimmiyar rawa da kungiyar tarayyar Turai ta taka a wasu fannoni. Da ya ke hadin kan Turai da Amurka ya karu, banbancin dake tsakaninsu kan wasu batutuwa ya fito fili.musamman kan rikicin kudi. Mr Shi Yinghong yana mai ra'ayin cewa moriyar Amurka da ta Turai ta sha banban da juna, da wuyan a daidaita sabanin dake tsakaninsu. Ya ce "bayan da aka samu rikicin kudi da tabarbarewar tattalin arziki,moriyar Amurka da ta Turai sun sha banban da juna kan yadda aka warware matsalolin da ake fama da su, ko ma a taron koli na London matsayinsu ma ya banbanta,sabanin dake tsakaninsu ba karamin abu ba ne. Obama ya dora muhimmanci kan sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki,amma a hakika ya kauce wa tsarin kudi na duniya na wall street da Amurka ke jagoranta da Turawa suke so a sa ido a kai. Shi ya sa kungiyar tarayyar Turai ba ta jin dadi da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka ba. Ta kuma fito fili ta kai suka ga gwamnatin Amurka,ta kumma bayyana matsayinta da ya sha banban da na Amurka."

Matakin da shugaba Obama ya bayyana kan shirin Amurka na girke na'urorin kakkabe makami mai limzani a kasar Czeck,wani muhimmin batu ne a gun taron koli. Obama ya bayyana cewa idan Iran ba ta yi rangwame kan shirinta na nukiliya ba, Amurka ta ci gaba da girke na'urorinta na kakkabe makami mai limzani a Turai ta gabas. Mr Shi Yinghong ya bayyana cewa kan batun girke makamai na kakkabe makami mai limzami,matakin da gwamnatin Obama ya dauka a yanzu ya tashi kusan daya da na Turai, dukkansu sun dora muhimmanci kan moriyar Rasha."Idan aka yi la'akarin da fargaba da ke akwai da Iran ta iya kera makaman kare dangi a nan gaba, babu shakka Amurka za ta yi kokarin tabbatar da shirinta na girke na'urori na kakkabe makami mai linzami a Turai ta gabas. Amma Amurka tana da tata moriya,wato tana so ta sassanta dangantaka dake tsakaninta da Rasha mai karfi a fannin soja."

1 2 3