
A ran 5 ga wata da yamma aka kammala taron koli na tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Amurka a Prague,babban birni na kasar Czeck.wannan ne karo na farko da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyanu a taron koli na nahiyar Turai da Amurka. An tattauna kan yadda za a inganta dangantakar dake tsakanin nahiyar Turai da Amurka da kuma karfafa hadin kan bangarori biyu kan muhimman batutuwan duniya. Yayin da Mr Shi Yinghong,darekatan cibiyar nazarin harkokin Amurka ta jami'ar jama'a ta kasar Sin ke hira da wakilin gidan rediyo na kasar Sin, ya bayyana cewa gwamnatin Obama tana da nufin tabbas na inganta dangantaka dake tsakanin Amurka da nahiyar Turai,duk da haka yayin da halin da tabarbarwar hada hada kudi da duniya ta shiga a ciki a yanzu da kuma kowanensu ya yi la'akari da moriyarsa kawai, da wuyan Obama ya dauki matakai masu amfani, shi ya sa dangantakar dake tsakanin nahiyar Turai da Amurka ta ci gaba tare da rashin sanin tabbas.
1 2 3
|