Gyare-gyaren dimokuradiyya ya sa miliyoyin bayi manoma sun samu 'yanci, kuma sun samu sabon zaman rayuwarsu. Sakataren reshen Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a jihar Tibet Zhang Qingli ya ce, 'A hakika dai, gyare-gyaren ya soke tsarin bauta na gargajiya, da kuma 'yantar da miliyoyin bayi manoma a jihar Tibet, ya kasance da muhimmiyar alama ga ayyukan soke tsarin bauta na duniya, shi ne kuma babban ci gaba da aka samu ta fuskar sha'anin kiyaye hakkin bil Adam na duniya. Kazalika kuma, shi ne muhimmin taimakon da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da jama'ar kasar suka bayar kan ayyukan dimokuradiyya, da 'yancin kai, da hakkin bil Adam na duniya. Gaskiya ne, yana da ma'ana sosai a tarihin bunkasuwar jihar Tibet, da tarihin zamani na kasar Sin, da tarihin bunkasuwar zaman al'umma na dan Adam.'
A cikin shekaru 50 da aka yi gyare-gyaren dimokuradiyya, an samu manyan sauye-sauye a jihar Tibet. Tsondre, wanda ya taba zama bawa manomi a da, ya bayyana cewa, 'Garinmu ya samu sauye-sauye sosai a cikin wadannan shekaru 50, zaman rayuwar jama'a na kara samun kyautatuwa. Mun samu hanyoyin mota, da talibijin, da sabbin gidaje, da kudi, kuma dukkan yaran ke iya shiga makaranta.'
1 2 3
|