A watan Janairu na shekarar bana, majalisar walikan jama'ar jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta zartas da wani kuduri, inda aka mayar da ranar 28 ga watan Maris a ko wace shekara da ta zama 'Ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet', don tunawa da gyare-gyaren dimokuradiyya da aka yi a shekaru 50 da suka wuce. Yau ranar 28 ga wata, 'Ranar tunawa da cika shekaru 50 da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet' ta farko ce, a gun bikin taya murnar ranar da aka shirya a birnin Lhasa, sakataren reshen Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a jihar Tibet Zhang Qingli ya bayyana cewa, a cikin wadannan shekaru 50 da suka wuce, an samu sauye-sauye sosai a jihar Tibet, jama'ar jihar suna zaman alheri. Nan gaba kuma, za a ci gaba da inganta babbar bunkasuwar tattalin arziki a jihar Tibet, ya zuwa shekarar 2020 kuma, za a tabbatar da kafa tushen raya zaman al'umma mai wadata a dukkan fannoni a jihar.
Wakilai fiye da dubu 13 da suka zo daga kabilu da bangarori daban daban na jihar Tibet sun halarci wannan bikin taya murna da aka shirya a ranar 28 ga watan Maris. A matsayinsa na wakilin miliyoyin bayi manoma a Tibet, Tsondre, 'dan shekaru 69 ya yi jawabi cewa, A tsohuwar Tibet, miliyoyin bayi manoma kamar ni sun yi zama daga zuriyoyi a karkashin ci da gumi da iyayen gijinsu suka yi musu.'
1 2 3
|