Baya ga bunkasa sha'anin yawon shakatawa na gargajiya, a cikin 'yan shekarun nan, jihar Tibet tana kokarin raya harkokin yawon shakatawa a yankunan halittu masu rai, ciki har da filayen noma da yankunan kiwon dabbobi. A yankin Nyingchi na jihar, akwai wani karamin kauye mai suna Namse, wanda ke samun bunkasuwa sosai sakamakon sha'anin yawon shakatawa. Mataimakin shugaban kauyen Mista Nyima ya ce: "Mazauna kauyenmu sun gina dakuna da dama, don gudanar da harkoki daban-daban, ciki har da sayar da tsarabobi na wurinmu, da bude gidajen cin abinci, da sayar da kayayyakin kimiyya da fasaha na gargajiya, da dai sauran makamantansu. Yawan kudin shiga da muke samu daga sha'anin yawon shakatawa ya kai kashi 70 bisa dari."(Murtala) 1 2 3
|