Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-27 19:32:32    
Sha'anin yawon shakatawa a jihar Tibet yana taimakawa ci gaban tattalin arzikin jihar

cri

Sakamakon dadadden tarihi, da kyawawan al'adun gargajiya, gami da ni'imtattun wurare daban-daban, jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta dade tana kasancewa wani sashin dake jawo hankalin masu yawon shakatawa daga dukkan duniya. Bayan da aka kaddamar da hanyar dogo da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet a watan Yuli na shekara ta 2006, sha'anin yawon shakatawa na jihar yana samun bunkasuwa sosai, wanda kuma ke taimakawa ci gaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar mazauna wurin.

Baya ga wuraren ibada masu tsawon tarihi na addinin Buddah da kyan yanayin wurin, kayayyakin kimiyya da fasaha masu salon musamman na kabilar Tibet suna jawo hankalin masu yawon shakatawa. Dardumar kabilar Tibet tana daya daga cikin kyawawan kayayyakin kimiyya da fasaha na gargajiya na jihar Tibet.

1 2 3