Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-27 19:32:32    
Sha'anin yawon shakatawa a jihar Tibet yana taimakawa ci gaban tattalin arzikin jihar

cri

A masana'antar samar da darduma ta gundumar Chengguan ta birnin Lhasa, mai taimakawa shugaban masana'antar Madam Dekyi Drolkar ta ce, dardumar gargajiya da ake samarwa a masana'antar tana ta kara samun karbuwa daga masu yawon shakatawa, inda ta ce:"Muna nacewa ga bin fasahohin gargajiya da yin amfani da ulu a yayin da muke saka darduma. Muna maida hankali sosai kan tsara fasalin zane-zanen dake kan dardumar, ciki har da zane-zanen gargajiya na kabilar Tibet, da kuma na zamani."

Baya ga dardumar kabilar Tibet, wasu fasahohin gargajiya, ciki har da fasahar samar da kayan alatu na gargajiya, da wukar gargajiya, suna cin gajiya sosai daga bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa a jihar. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, adadin masana'antun samar da kayayyakin kimiyya da fasaha na kabilar Tibet ya zarce dari, wadanda ke bayar da babbar gudummawa ga habakar tattalin azikin jihar.

A halin da ake ciki yanzu, akwai kuma hanyoyi da dama wadanda jama'ar jihar Tibet suke bi wajen cin gajiya daga sha'anin yawon shakatawa, ciki har da kaddamar da otel-otel asu sigar musamman ta kabilar Tibet. Otel din Tenzin, wani otel ne mai zaman kansa wanda ya yi suna sosai a birnin Shigatse na jihar. Yanzu, wannan otel yana jawo hankalin masu yawon shakatawa da yawa daga sassa daban-daban na duniya. Darektar otel din Madam Sodron ta ce, an kaddamar da otel din ne a farkon lokacin da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. A lokacin, sannu a hankali ne aka samu wasu masu yawon bude ido wadanda suka je jihar don yin bulaguro, shi ya sa mahaifinta ya bude wannan otel. Madam Sodron ta ce: "A lokacin, mahaifina yana gudanar da harkokin ciniki, akwai mu'amala da cudanya a tsakaninsa da 'yan kasar Nepal. Shi ya sa ya sami ra'ayi na bude wani otel."

1 2 3