Amma matarsa Huang Ruiwo ba ta nuna goyon baya ga shirinsa ba. Bayan Shen Yiyao ya lallashe ta, ta amince da yin wannan ziyara a karshe. Amma, Huang Ruiwo ba ta yi tsammanin jin dadin ziyararsu a jihar Tibet sosai ba. Ta ce, "Akwai abinci iri iri masu dadin ci a otel da muke zama. Mutanen jihar Tibet sun nuna maraba sosai ga baki, kuma akwai yara masu fara'a a jihar, na dauki wani hoto ga yara guda biyu da Shen Yiyao, yaran suna rera wakoki suna rawa."
A lokacin zaiyarar mako guda, Shen Yiyao da matarsa sun kai ziyara a biranen Lahasa da Zedang da Jiangzi da kuma Rikazr da dai sauransu, kuma sun ziyarci wasu shahararrun wuraren yawon shakatawa. Shen Yiyao ya ce, "A da, babu hanyar jirgin kasa a jihar, amma yanzu, an shimfida hanyoyin jirgin kasa, jihar Tibet ta samu bunkasuwa cikin gaggawa."
Shen Yiyao da matarsa sun gamu da masu yawon shakatawa daga kasashen Turai wadanda suka nuna babban yabo ga jihar Tibet. Huang Ruiwo ta ce, "Kungiyar masu yawon shakatawa ta Turai suna tsammani cewa, jihar Tibet tana kama da Aljanna a duniya. Ba za a samu matsala ba idan ana jin Turanci, sabo da galibin mutanen jihar Tibet suna iya Turanci."
1 2 3
|