Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-27 15:22:39    
Kaddarar dake tsakanin wani Basine mazaunin kasar Amurka da matarsa da jihar Tibet

cri

Shehun malami Shen Yiyao wanda ke zama a kasar Amurka har shekaru 50 ko fiye shi ne wani shahararren Basine shehun malami a yankin Washington, kuma matarsa Huang Ruiwo ita ce Basiniya da aka haife ta a kasar Indonesia. Sabo da wani labarin da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka bayar kan jihar Tibet, Shen Yiyao da matarsa da ba su fahimci jihar Tiber sosai ba sun yi niyar kawo ziyara a jihar don yin bincike. Amma, daga nan ne, suka nuna sha'awa sosai ga wannan jihar, kuma suna kaunar yanayin dabi'u da al'adun wannan jiha. Daga baya, sun rika yin nazari kan jihar Tiber har na tsawon shekaru fiye da 10. Yanzu, ga bayanin da wakiliyarmu Wang Shanshan dake kasar Amurka ta ruwaito mana.

Shehun malami Shen Yiyao mai shekaru 82 da haihuwa yana yin bincike kan tarihin Sinawa mazauna kasashen waje. Ya yi aikin ba da ilmi a yankin Taiwan bayan ya gama karatu a jami'ar Zhongshan dake lardin Guangdong. A shekarar 1957, ya je kasar Amurka don karatu, daga baya, ya yi aiki a jami'ar Maryland da dakin ajiye litattafai na majalisar ministoci ta kasar Amuka da kuma jami'ar Columbia. A shekarun da suka gabata, yana yin aikin nazari kan jihar Tibet. Shen Yiyao ya ce, yana mai sha'awar jihar Tibet sabo da wani labarin da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka bayar. Ya kara da cewa, "A wancan lokaci, labarun kasar Amurka sun yi ikirarin cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin ta kashe mutane miliyan guda na jihar Tibet. Amma ban amince da wadannan labaru ba, na samu rahoto cewa, yawan mutanen jihar Tibet ya kai miliyan guda kawai a shekarar 1950, shin ko dukkan mutanen jihar Tibet sun mutu? Sabo da haka, na yi niyar kawo ziyara a jihar don yin bincike kan wannan lamari ni da kaina."

1 2 3