
Bugu da kari kuma, a kwanan baya, Mr. Donald Kaberuka, shugaban bankin raya Afirka ya kuma yi kira cewa, kada a manta da kasashen Afirka lokacin da ake tinkarar matsalar kudi ta duniya. Ya kuma nuna cewa, bai kamata a yi watsi da kasashen Afirka ba a gun taron koli na sha'anin kudi na kungiyar kasashe 20. Ya kamata kasashen Afirka su halarci taron tattaunawa kan batun tinkarar matsalar kudi ta duniya kamar yadda ya kamata, a cewar Kaberuka. (Sanusi Chen) 1 2 3
|