Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-27 10:37:18    
Kasashen Afirka suna sa rai ga taron koli na sha'anin kudi na G20

cri

A gun taron koli na sha'anin kudi na kungiyar kasashe 20, wato G20 da za a yi a birnin London na kasar Britaniya, muhimman kasashe masu arziki da wasu kasashe masu tasowa za su kara mai da hankali kan batun tinkarar matsalar kudi ta duniya. Ya kasance tamkar nahiya mafi fama da talauci da ke kunshe da kasashe marasa arziki mafi yawa, kuma ke fuskantar illa mafi tsanani da wannan matsalar kudi ta duniya ke kawo mata, nahiyar Afirka tana fatan a gun wannan taron koli na sha'anin kudi, kasashe masu arziki za su iya cika alkawarinsu na bai wa kasashen Afirka tallafin kudi na neman ci gaba. A waje daya, kasashen Afirka sun nemi a kara sa ido kan tsarin sha'anin kudi na duniya da kuma yin kwaskwarima kan asusun ba da lamuni na duniya, har ma za su iya nuna wa kasashen Afirka karin goyon baya. Bugu da kari kuma, kasashen Afirka suna fatan shirin sa kaimi kan tattalin arziki da kasashen yammacin duniya suke aiwatarwa zai iya rage illar da matsalar kudi ta duniya ke kawo wa kasashen Afirka.

Yanzu illar da matsalar kudi ta duniya wadda ta zama annoba a duk duniya, kuma ke kawo wa kasashen Afirka wadanda suke kudu da hamadan Sahara tana tsananta sannu a hankali. Bisa labarin da aka bayar, an ce, a kwanan baya, shugabanni da ministocin kudi na wasu kasashen Afirka sun yi taro a birnin London da Gordan Brown, firayin ministan kasar Britaniya. Bayan wannan taro, Mr. Raila Odinga, firayin ministan kasar Kenya ya ce, yanzu farashin kayayyakin masarufi na Afirka ya ragu sakamakon raguwar bukatun da ake nema a kasuwannin kasashen duniya. Kuma yawan masu yawon shakatawa da suke zuwa Afirka yana ta raguwa. Sakamakon haka, yawan kudaden musaya da jarin waje sun ragu. Kasashen Afirka sun riga sun gane cewa, kamar yadda sauran nahiyoyin duniya suke fuskanta, nahiyar Afirka tana kuma shan wahalar wannan matsalar kudi ta duniya. Ko da yake a gun taron koli na sha'anin kudi na kungiyar kasashe 20, batun Afirka ba zai jawo hankalin mutane sosai ba, amma, tabbas ne zai zama daya daga cikin batutuwan da za a tattauna.

1 2 3