Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-27 10:37:18    
Kasashen Afirka suna sa rai ga taron koli na sha'anin kudi na G20

cri

Yanzu shugabannin kasashen Afirka sun amince da shawarar "kafa wani asusun taimakawa kasashe marasa karfi" da Mr. Robert Zoellick, shugaban bankin duniya ya bayar. Wadannan shugabannin kasashen Afirka sun yi kira ga kasashe masu arziki da su samar da wasu kudade ga wannan asusu domin taimakawa kasashen Afirka da tattalin arzikinsu yake cikin mawuyacin hali sakamakon matsalar kudi ta duniya. Kasashen Afirka sun kuma yi fatan cewa, dole ne kasashe masu arziki sun ba su sabon tallafin kudi, amma ba tallafin kudin da suka dauki alkawarin cewa za su samar wa kasashen Afirka ba.

A cikin dukkan kasashen Afirka, kasar Afirka ta kudu kawai za ta halarci wannan taron koli na sha'anin kudi na kungiyar kasashe 20 da za a yi a birnin London na kasar Britaniya a madadin wakilin kungiyar. Sannan, bisa gayyatar da aka yi musu, Mr. Meles Zenawi, firayin ministan kasar Habasha da Mr. Jean Ping, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka za su halarci wannan taro a madadin kasashen Afirka. Har sau da yawa ne kungiyar tarayyar Afirka ta riga ta bayyana cewa, lokacin da ake tinkarar matsalar kudi ta duniya da yin gyare-gyare kan tsarin sha'anin kudi na duniya, ya kamata a kara wakilci da ikon magana na kasashen Afirka.

1 2 3