Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-26 18:42:27    
Kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa na kokarin neman hanyoyin tinkarar matsalar kudi

cri

A gaban matsalar kudi, kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa na fuskantar matsaloli daban daban sabo da halin da suke ciki daban daban ne, amma babu shakka, ya zama dole a inganta hadin kai a tsakanin kasa da kasa. A yayin da ya tabo magana a kan tabbatar da karfin karuwar tattalin arzikin nahiyar Asiya, J.T.Jaboc, masanin ilmin tattalin arzikin Indiya ya ce,"Kasancewarsu manyan kasashe a nahiyar Asiya, ya zama dole Sin da Indiya su hada kansu da kuma tallafawa juna a halin da ake ciki, inda ba haka ba, za su yi fama da illar da rikicin hada hadar kudi ke iya haddasa musu."

Luis Alberto Bussio, shugaban hadaddiyar kungiyar kasuwanci tsakanin Argentina da Sin, yana ganin cewa, inganta hadin kai tsakanin shiyya shiyya yana da muhimmanci sosai, ya ce,"Ya kamata Argentina ta inganta huldar cinikayya tsakaninta da sauran kasashen Latin Amurka, misali, muna hulda sosai da Brazil ta fannin siyasa, amma ba a bunkasa bangaren ciniki sosai ba. Ko da yake Argentina ta yi kokari sosai ta fannin kungiyar kasuwar bai daya ta Mercosur, amma ba mu yi cikakken amfani da fifikon kasuwar ba tukuna, sabo da haka, kamata ya yi, Argentina ta kara kokari wajen bunkasa kasuwar."(Lubabatu)


1 2 3