A matsayinta na kasa mafi girma da tattalin arzikinta ke tasowa a nahiyar Latin Amurka, Brazil ta riga ta rage karuwar tattalin arzikinta a wannan shekara zuwa kashi 2%. A yayin da yake hira da wakilinmu, mashahurin masanin ilmin tattalin arziki na kasar Brazil, Josue Souto Maior Mussalem ya ce, matsalar kudi kalubale ne da ke gaban kasashen duniya baki daya, kamata ya yi a dauki matakai kan tsarin kudi gaba daya, kamar yadda ya ce,"Da farko, ya kamata a farfado da inganci da aminci na tsarin kudin duniya, sa'an nan, a farfado da harkokin ba da lamuni da habaka kasuwannin duniya da kuma kawar da shingayen haraji da aka kafa ta fuskar cinikayyar duniya. Ban da wannan, ya kamata a sassauta damuwar jama'a da rashin aikin yi, wanda ya tsananta sakamakon matsalar tattalin arziki."
1 2 3
|