Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-26 18:42:27    
Kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa na kokarin neman hanyoyin tinkarar matsalar kudi

cri

Tun karshen shekarar 2008, tattalin arzikin kasashe masu karfin tattalin arziki kamar Amurka da Japan da Turai ya fara dakushewa sakamakon matsalar kudi ta duniya, haka kuma matsalar ta galabaitar da kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa, ciki har da Sin da Brazil da kuma Indiya. Wadannan kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa sun samar da kuzari sosai ga ci gaban tattalin arzikin duniya a 'yan shekarun baya, amma a mawuyacin halin da ake ciki yanzu, suna fuskantar babban kalubale, amma kuma suna kokarin neman hanyoyin tinkararsa.

A cikin 'yan shekarun baya, saurin karuwar tattalin arzikin kasashe masu tasowar ya jawo hankulan kasashen duniya, amma a sakamakon matsalar kudi, asusun ba da lamuni na duniya, wato IMF, ya yi hasashen cewa, a wannan shekarar, saurin karuwar tattalin arzikin kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa zai ragu daga kashi 6.3% na bara zuwa 3.3%. A cewar J.T.Jacob, babban manazarci kan harkokin tattalin arziki a cibiyar nazarin zaman lafiya ta Indiya, kamata ya yi Indiya da sauran kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa su yi kokarin daidaita tsarin tattalin arzikinsu, ya ce,"Sin da Amurka dukansu sun gyara tsarin tattalin arzikinsu domin fuskantar halin da ake ciki yanzu, sun kuma dauki matakai na samar da kuzari ga tattalin arziki. Domin tinkarar matsalar kudi, kamata ya yi kasashe daban daban su daidaita tsarin tattalin arzikin duniya."

1 2 3