Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-26 13:48:12    
Nune nunen hotunan da aka shirya kan ci gaban jihar Tibet ta kasar Sin

cri

" A da mun samu wasu labarai ne na game da jihar Tibet ta hanyar kallon sinima, labaran da muka samu ba na cikakku ba. Ga shi a yau na ziyarci nune nunen da aka shiyra, na gano ainihin cigaban jihar Tibet. Maganganu marasa gaskiya da rukunin Dalai Lama ya kan yi, a ganina suna tsoron abin gaskiya. Ina so in gaya wa jama'a cewa wasu labarun da kuka ji game da Tibet ba gaskiya ko kadan a ciki. Idan kana so ka ga ainihin halin da Tibet ke ciki,to kamar yadda na yi a yau ku zo da kanku ku ga hotuna da kayayyakin tarihi da takardun da aka baje kan ci gaban jihar Tibet."

A dakunan nune nunen, masana na cibiyar nazarin ilimin Tibet ta kasar Sin sun yi musayar ra'ayi da jakadun kasashen waje ta fuskar aminci da arziki, kuma cikin tsanaki sun amsa tambayoyin da suka yi musu,suka yi bayani kan manufar siyasa da gwamnatin kasar Sin ta ke bi kan jihar Tibet. Da hakikan abubuwa da adadai suka bayyana manyan nasarorin da aka samu a jihar Tibet a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma zamantakewa cikin shekaru hamsin da suka shige bayan da aka kawo sauyi ta hanyar demakuradiya. Alal misali kudin shiga na tsaraba na shekara na kowane manomi da makiyayi ya linka kusan sau dari bisa na shekara ta 1959, tsawon rai na kowae mutum ya karu daga shekaru 36 na da zuwa shekaru 67 da haihuwa a halin yanzu, kashi 98.5 bisa dari na 'yaran da suka isa shekarun shiga makarantun firamare sun shiga makarantunsu, kowane mutane dari na da wayoyinn tarho 55.

Jakadan kasar Cuba a Sin Carlos Miguel ya bayyana cewa nasarorin da aka samu a Tibet sun bayyana namijin kokarin da gwamnatin tsakiya na kasar Sin ta yi " bayann da na ziyarci nune nunen,abin da ya fi burge ni kuma in yi yabo a kai shi ne zaman mutnen jihar Tibet na samun ingantuwa sosai,aka kuma samu manyan sauey sauye bayan kafusar jamhuriyar jama'ar kasar Sin musamman a cikin shekaru talatin da suka shige bayan aka kawo sauyi da bude kofa, wannan ba ma kawai ya shaida kokarin da gwamnatin tsakiya ta yi domin bunkasa jihar Tibet ba, hatta ma ya shaida niyar gwamnatin tsakiya kan bunkasa jihar Tibet da kuma yadda gwamnatin tsakiya ta cika alkwaran da ta dauka."

1 2 3