A ran 25 ga wata da yamma, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta gayyaci jakadu na kasashen ketare da wakilan hukumomin duniya a Sin su sama da sittin sun ziyarci nune nunen hotunan da ake yi kan ci gaban da jihar Tibet ta samu bayan da ta yi gyare gyare ta hanyar demukuradiya. Bayan da aminanmu baki suka duba hotunan da aka baje,sun bayar da ra'ayoyinsu kan ci gaban da jihar Tibet ta samu.
An baje hotuna sama da dari biyar da kayayyakin tarihi da takardu fiye da 180 a nune-nunen, ta haka aka bayyanawa maziyararta halin koma baya da duhu da manoma bayi ke ciki a zamanin da a jihar Tibet,aka bayyana ainihin tarihi kan yadda rukunin Dalai Lama ya kaddamar da bore da makamai a shekara ta 1959, haka kuma aka bayyana ci gaban da bunkasuwa da jihar Tibet ta samu cikin shekaru hamsin da suka gabata bayan da aka yi mata gyare gyare ta hanyar demakuradiya, da hakikanan abubuwa aka karyatar da jita jita da rukunin Dalai Lama ya baza na wai "matsalar Tibet"
Akwasi Agyeman Agyare,wakilin kasar Ghana a matsayin jakada a Sin yana mai ra'ayi cewa bayyana ci gaban da jihar Tibet ta samu ta nune-nunen da ake yi,wata kyakyawar hanya ce, ta nune nunen, mutane na iya gane me ya faru a jihar Tibet cikin shekaru hamsin a suka gabata.
1 2 3
|