Daga baya kuma Mr. Rajoelina ya duba faretin sojoji na girmamawa na sama da na ruwa da kuma na kasa, kana kuma ya yi jawabi kan kama aiki, inda ya bayyana cewa, bayan da ya kama aiki, zai mayar da batun kawar da talauci da kyautata zaman rayuwar jama'a a gaban dukkan manufofi. Kuma ya kara da cewa, "Sabuwar gwamnati za ta ba da tabbaci ga muradun jama'ar kasar Madagascar, da farko za mu kebe kudaden gwamnatin cikin ayyukan ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma domin kyautata zaman rayuwar jama'a."
A gun bikin kama aiki da aka shirya a ran nan, ba a samu halartar jakadun kasashe da ke kasar Madagascar da kuma wakilan kungiyoyin shiyya shiyya da na duniya ba. Kasashen duniya sun mayar da martani sosai kan yadda Mr. Rajoelina ya zama shugaban kasar Madagascar. A idanun kungiyar tarayyar Afirka da kungiyar tarayyar Turai da dai sauran kungiyoyin duniya da kuma kasashen Amurka da Faransa da dai sauransu, wannan juyin mulki ne da ya faru a kasar, kuma sun bukaci kasar Madagascar da ta shirya babban zabe tun da wuri. Game da wannan, Mr. Rajoelina ya bayyana cewa, zai tabbatar da zaman lafiyar jakadun kasashe da ke kasar da kuma ma'aikatan kungiyoyin duniya, kuma ya yi alkawarin cewar, za a zartas da sabon tsarin mulkin kasar da kuma shirya babban zabe a cikin shekaru biyu masu zuwa. Ban da wannan kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su amince da halin siyasa da Madagascar ke ciki yanzu. Ya ce, "Jama'a na kasashe daban daban da dukkan kasashe masu sada zumunci tare da mu da kuma masu ba mu taimako, na yi muku alkawari a tsanake kan cewa, kasar Madagascar za ta ci gaba da sada zumunci tare da dukkan kasashe da jama'a na duniya."
1 2 3
|