A ran 21 ga wata, Andry Rajoelina ya yi ratsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Madagascar a filin wasanni mafi girma da ke cikin Antananarivo, babban birnin kasar. Mutane kusan dubu 50 da ke goyon bayan Mr. Rajoelina sun je filin don kallon bikin kama aiki tare da yin kirari da kuma daga hotunan Rajoelina sama.
A ran nan da karfe 12 da minti 5 na tsakar rana bisa agogon wurin, an kaddamar da bikin kama aiki ta hanyar yin kide-kide da 'yan badujala suka yi. Kuma a gaban idon Jean Rajaonarivony, babban alkali na kotun koli ta tsarin mulkin kasar, Mr. Rajoelina ya sa lamba mai daraja da kuma janjami mai nuna girmamawa da ke wakiltar ikon shugaban kasar, da kuma yin rantsuwa tare da daga hannunsa na dama, yana fadin cewar "Na yi rantsuwa a gaban jama'ar kasar Madagascar da kuma Allah, wato zan yi iyakacin kokarina domin kawo wa jama'ar kasar alheri, a waje daya kuma zan nuna girmamawa ga dokokin kasar Madagascar."
1 2 3
|