Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-19 21:19:09    
Horaswa da aka shirya don manoma ya sa kaimi sosai ga ayyukan cin rani na jihar Ningxia

cri

Ma Yahong mai shekaru 20 da haihuwa ta taba shiga kwas din koyar da ilmin kwamfuta na tsawon rabin shekara guda a shekara ta 2007, daga baya kuma ta je birnin Suzhou da ke gabashin kasar Sin don yin aikin ci rani, yawan kudaden da take samu a ko wane wata ya kai Yuan 1400. Amma Ma Yahong ba ta gamsu da wannan aikin da ba shi da fasaha ko kadan ba, shi ya sa ta bar shi, ta kuma sake shiga makarantar koyar da ilmin kwamfuta ta Qingsong ta birnin Yinchuan domin ci gaba da karatunta. Ma Yahong ta gaya mana cewa,"Na iya samun kudi da yawa lokacin da nake yin aikin cin rani a birnin Suzhou, amma aikin da na gudanar ba shi da fasaha sosai, shi ya sa bayan da na samu kudi, na dawo domin ci gaba da karatu. Bayan da na kara ilmin fasahohi, to zan iya samu gurbin aikin yi a fannoni daban daban. Ban da wannan kuma in na samu ilmin fasahohi, to zan iya raya aikina a maimakon gudanar da aiki don sauran mutane kawai."

Chen Xiaojun, shugaban ofishin kula da harkokin 'yan kwadago na hukumar tabbatar da samun guraban aikin yi ta jihar Ningxia ya bayyana cewa, yanzu yawan manoman jihar da ke da ilmin fasahohin sana'o'i ya kan karu da kashi 16 cikin kashi dari a ko wace shekara, kuma kudin da manoma su kan samu ta hanyar cin rani ya riga ya kai kusan rabi daga cikin dukkan kudaden da suke samu. Kuma ya kara da cewa, "yanzu aikin cin rani na jihar Ningxia ya riga ya zama wata sabuwar hanya ga manoma wajen sauya hanyoyin samun guraban aikin yi bisa kwarewarsu da kuma ilminsu. Sabo da haka ya samar da wani dandali wajen kafa kasuwar bai daya a fannin samar da guraban aikin yi ga masu aikin yi na birane da na kauyuka."

To, masu sauraro, shirinmu na yau na "Zaman rayuwar musulmai na kasar Sin" ke nan. Da fatan kun karu, da haka Kande da ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Kande Gao)


1 2 3