Daga shekara ta 2005, jihar Ningxia ta kaddamar da aikin horar da manoma miliyan guda daga dukkan fannoni, wato gwamnatin jihar ta kebe kudin musamman don ba da rangwame, hukumomin shirya ayyukan horaswa kuma sun horar da manoma bisa bukatun kasuwa, haka kuma kamfanoni sun zabi wasu nagartattun mutane wajen samar da guraban aikin yi. Ta wannan hanya, an samar da dimbin manoma da ke da ilmi da kuma fasaha. Chen Xiaojun, shugaban ofishin kula da harkokin 'yan kwadago na hukumar tabbatar da samun guraban aikin yi ta jihar Ningxia ya bayyana cewa,"Matsakacin yawan kudin da manoma masu cin rani na jihar Ningxia suka samu a shekara ta 2006 ya kai kashi 60 cikin dari bisa na duk kasar Sin, wannan ya shaida cewa, ko da yake manoman da suka yi aikin cin rani na jiharmu suna da yawa, amma suna karancin fasahohin ayyuka, shi ya sa ba su iya samun dimbin kudaden shiga ba. Sabo da haka mun kara karfin ayyukan horaswa, gwamnatin jihar tana kebe kudaden Sin har Yuan miliyan 30 a ko wace shekara domin kyautata fasahohin manoma."
Abin da kuka saurara dazun nan amo ne kan yadda malamin horaswa ke koyar da ilmin kwamfuta ga manoma na kauyen Tonggui na unguwar Xingqing ta birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia. A cikin wani ajin horaswa da cike da mutane, wakilinmu ya gano cewa, malamin yana yin bayani kan shafin rubutu ko 'word' da ke cikin kwamfuta, kuma manoma da ke gaban kwamfuta suna mai da hankali sosai wajen karatu.
Duan Xueqing, wata manomiya ce musulma ta kauyen Tonggui mai shekaru 34 da haihuwa ta riga ta haifi yara biyu, ko da yake ta kan sha aikin gida sosai, amma tana tsayawa tsayin daka kan koyon ilmin kwamfuta. Ta gaya wa wakilinmu cewa, "In an samu ilmi, tabbas ne za a yi amfani da shi. A cikin manoma, kullum mata ba su da aikin yi. Ina ganin cewa, idan na iya kwamfuta, da farko na iya koyar da yarana, ban da wannan kuma ba zan iya zuwa waje don yin aikin cin rani ba sai dai na samu ilmi. In ba a samu fasaha ba, to ba zai yiwu a samu guraban aikin yi ba."
1 2 3
|