Bisa labarin da muka samu, an ce, ban da ilmin kwamfuta, ana koyar da fasahohin gine-gine da ayyukan wutar lantarki da yin takalma da tufafi a cibiyar horaswa, shi ya sa ayyukan horaswa sun samu amincewa sosai daga fararen hula.
Jiang Hongtao, shugaban hukumar kula da samar da guraban aikin yi ta unguwar Xingqing ya gaya mana cewa, a shekaru 3 da suka gabata, unguwar Xingqing ta horar da manoma 'yan cin rani dubu 30, kuma kashi 85 cikin kashi dari daga cikinsu sun samu takardun gama kataru, haka kuma an gabatar da kashi 82 cikin kashi dari daga cikinsu wajen samun guraban aikin yi. Manoma sun shiga kwasa-kwasan horar da fasahohin sana'o'i da suke sha'awa ba tare da biyan ko kwabo ba, kuma za a gabatar da su wajen samun guraban aikin yi bayan da suka samu takardun gama karatu, irin wannan tsari ya kara kwarin gwiwar dimbin manoma wajen shiga kwasa-kwasan. Kuma Mr. Jiang ya bayyana cewa,"Yawancin manoma sun shiga ayyukan horaswa bisa zabinsu. A lokacin da, fararen hula ba su samu takardun fasaha ba, shi ya sa kullum su kan samu kudaden shiga kadan lokacin da suke yin aikin cin rani. Amma bayan da suka shiga ayyukan horaswa, fasahohin da suke iya samu sun samu kyautatuwa, kuma yawan kudin shiga da suka samu ya karu, lalle mamoma sun samu alheri sosai."
Duan Hongfu, wani manomi ne musulmi na kauyen Tonggui na unguwar Xingqing, yanzu shekarunsa sun kai 40 da haihuwa, a lokacin sararawar aikin gona na lokacin hunturu, ya kan gudanar da aikin kula da na'urar dumama daki. Amma sabo da ba shi da takardar fasahar gudanar da aikin, shi ya sa yawan kudaden da yake samu a ko wane wata bai wuce Yuan dari uku kawai ba. A watan Maris na shekarar ta 2007, ya shiga kwas din horar da fasahar kula da na'urar dumama daki, kuma ya samu takardar fasahar ta matakin farko. Sabo da haka, yawan kudaden da ya samu a lokacin hunturu da ya gabata ya ninka kusan sau hudu. Lokacin da yake tabo maganar alherin da kwas din horaswa ya kawo masa, Duan Hongfu ya ce,"In ba ka da takardar fasahar gudanar da aiki, to ba za a dauke ka ba. Bayan da na samu takardar fasaha, samun gurbin aikin yi ya zaman tamkar abu mai sauki, kuma yawan kudaden da na samu ya karu sosai. Lokacin da na fara gudanar da wannan aiki, na iya samu Yuan dari uku ne kawai a ko wane wata, amma yanzu wannan jimilla ta zarce Yuan dari 8, ta haka zaman rayuwata ya samu kyautatuwa sosai."
Ba kawai kwasa-kwasan horar da fasahohi sun tallafa wa dimbin manoma wajen samun guraban aikin yi na fasaha a maimakon yin amfani da karfi kawai ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne manoman sun bude idanunsu da kuma canja ra'ayoyinsu, ta haka sun fahimci muhimmancin ilmi da fasaha sosai. Bisa labarin da muka samu, an ce, manoma 'yan ci rani da yawansu ya kai kashi 40 cikin kashi dari da suka taba shiga kwasa-kwasan horaswa sun sake shiga kwasa-kwasan domin kara fasahohin da suke da su. Ma Yahong, wata manomiya ce musulma ta kauyen Qiying na gundumar Haiyuan ta birnin Guyuan tana daya daga cikinsu.
1 2 3
|