An labarta cewa, a duk tsawon lokacin da ake gudanar bikin shekarar sada zumunta tsakanin Sin da Korea ta Arewa, bangarorin biyu za su gudanar da harkoki iri dabam-daban kimanin 60 a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu, da wasannin motsa jiki, da kimiyya da fasaha da kuma na tarbiyya da dai sauransu. Ban da wannan kuma, za a gudanar da harkoki iri dabam-daban na musanye-musanye da sada zumunci a kowane wata. A yi gadon abubuwan gargajiya da inganta zumunci, da habaka musanye-musanye da hadin gwiwa da kuma ci gaba cikin kafada da kafada da kirkiro kyakkyawan makoma, manyan muradai uku ne na gududanar da shagalin shekarar sada zumunta. Firaminista Wen Jiabo ya bada karin bayani kan lamarin, inda ya furta cewa : ' Gudanar da bikin shekarar sada zumunta daidai a albarkacin cikon shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Korea ta Arewa na da muhmmmancin gaske. Na yi imanin cewa, bisa kokarin da bangarorin biyu suke yi, za a iya cimma kyakkyawan burin gudanar da irin wannan biki kamar yadda aka zata a da'. ( Sani Wang ) 1 2 3
|