Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-19 10:46:09    
Firayiministocin kasashen Sin da Korea ta Arewa sun halarci bikin bude ' Shekarar sada zumunta tsakanin Sin da Korea ta Arewa'

cri

An gudanar da bikin bude ' Shekarar sada zumunta tsakani kasashen Sin da Korea ta Arewa a jiya Laraba da dare a nan birnin Beijing. Firayiministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao da takwaran aikinsa na majalisar ministocin Korea ta Arewa Mista Kim Yong Il dake yin ziyara a kasar Sin sun halarci bikin budewa, inda bangororin biyu gaba dayansu suka bayyana kyakkyawan burinsu na ingiza yunkurin dinga inganta zumuncin gargajiya dake kasancewa tsakanin kasashen biyu. Shekarar bana, shekara ce ta cikon shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Korea ta Arewa. In ba a manta ba, tuni a ranar 1 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, shugabannin koli na kasashen biyu wato su Hu Jintao da Kim Jong-Il sun aike wa juna sakon taya murna, inda suka yi shelar soma gudanar da bikin ' Shekarar sada zumunta tsakanin Sin da Korea ta Arewa 'a hukumance. A gun bikin bude shekarar sada zumunta, an nuna wasannin fasaha masu ban sha'awa,wadanda aka rada musu sunan ' Buga take ga zumunci'. Kafin nuna wasannin, firaministan kasar Sin Mista Wen Jiabao ya yi jawabin fatan alheri don nuna babban yabo ga zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Korea ta Arewa . Yana mai cewa : 'Kasashen Sin da Korea ta Arewa, kyakkyawan kasashe makwabta ne hade da koguna da tsaunuka ; kuma ya kasance da zurfaffen aminci tsakanin jama'ar kasashen biyu. Tun da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin Jamhuriyar Jama'ar Sin da Jamhuriyar Jama'ar Demokuradiyya ta Korea cikin shekaru 60 da suka gabata, da karfi ne kasashen biyu suka ingiza bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma na bangarorin biyu, da taka mihimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na Zirin Korea har ma da na yankin arewa maso gabashin Asiya'.

1 2 3