Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-18 08:44:44    
Ana gudanar da aikin share fage na gasar wasannin Asiya ta Guangzhou yadda ya kamata

cri

Kan batun zuba jari, lallai za a tuna da rikicin kudi da ya barke a duk duniya yanzu, a karkashin irin wannan hali, ko shakka babu, kasa mai saukar baki tana fuskantar kalubale mai tsanani. Wasu manyan kamfanonin duniya sun canja tunanin zuba jari, amma gwamnatin Guangzhou da kwamitin shirya gasar wasannin Asiya suna yin kokari domin neman samun sabon iznin raya kasuwa. Kawo yanzu, sun riga sun samu abokan hadin gwiwa da yawan gaske. Abu mafi faranta ran mutane shi ne a ran 1 ga watan Fabrairu na bana, an daddale yarjejeniyar mikawar ikon raya kasuwa na zama na 16 na gasar wasannin Asiya a Guangzhou. Wannan ya alamanta cewa, a karo na farko cikin tarihin gasar wasannin Asiya, majalisar wasannin Olimpic ta Asiya ta mika wa birni mai shirya gasar ikon raya kasuwa daga duk fannoni. Haka shi ma ya nuna mana cewa, majalisar wasannin Olympic ta Asiya ta amince da kwamitin shirya gasar na Guangzhou sosai da sosai. Gu Shiyang ya bayyana cewa, jarin da aka samu ba ma kawai zai samar da isashen jari ga gasar wasannin Asiya ba, har ma zai ba da amfani ga gine-ginen birni cikin dogon lokaci.

Gu Shiyang ya ce:  "Don yin marhabin ga gasar wasannin Asiya, mun yi kokarin kyautata sufurinmu, musmaman sufuri a karkashin kasa, haka kuma za mu yi kokarin biyan bukatun 'yan kallo a yayin gasar. Ban da wannan kuma, muna yin kokarin gina hanyoyin mota da kuma kyautata muhallin halittu masu rai da marasa rai, lallai muna son biyan bukatun gasar yadda ya kamata."

Gu Shiyang ya kyautata tunani da cewa, tunanin gasar wasannin Olympic ta Beijing shi ne "sabon birnin Beijing, sabuwar gasar wasannin Olympic". Yanzu Guangzhou shi ma yana yin amfani da iznin domin kyautata kansa daga duk fannoni. (Jamila Zhou)


1 2 3